Monday, 25 December 2017

RIKICI YA YANKE A WANI YANKIN ABUJA

Wani rikici mai nasaba da kabilanci ya barke a garin Bwari da ke birnin tarayyar Najeriya, Abuja.
Rikicin dai ya barke ne bayan wasu da aka ce 'yan kungiyar asiri ne suka kai wani hari ranar Lahadi da daddare.
Wasu ganau sun shaida wa Arewapeople cewa harin ya yi sanadin mutuwar wani mutum.
Duk da cewar rikicin ya yi kamar ya kwanta daga ranar Lahadi zuwa safiyar Litinin, amma ya sake dawowa a ranar Litinin din inda aka yi ta afka wa juna tsakanin 'yan kabilar Gbagi (Gwarii) da Hausawa.
Wani mazaunin Bwari ya shaida wa Arewapeopl cewa an kona kusan rabin kasuwar Bwari.
Kasuwar kamar wata matattara ce inda kabilu daban-daban mafi yawa Hausawa da Igbo ke kasuwanci.
Nigeria: Zanga-zangar 'yan tasi ta tsayar da al'amura a Abuja
'Yan bindiga sun kai hari gidan shugaban EFCC Ibrahim Magu
Rundunar 'yan sanda a birnin Abuja ta tabbatarwa da Arewapeople cewa tuni ta baza jami'anta a garin na Bwari domin kwantar da rikicin.
Sai dai kakakin rundunar, Anjuguri Jesse Manzah, bai yi karin haske a kan adadin rayuka da kadarori da suka salwanta ba, yana mai cewa rundunar ta fi mayar hankali ne kan kokarin tabbatar da doka da oda kafin ta fara kididdigar abubuwan da aka rasa.
Kawo yanzu dai ba a san ainihin dalilin da ya kawo barkerwar wannan rikici ba, wanda kafin barkewar rikicin, mazauna yankin ke cewa ana zaune lafiya tsakanin kabilun da ke rayuwa a garin.

Thursday, 21 December 2017

Ashe ba a dakatar da Rahma sadau a kannywood ba

Rahama Sadau. Da zarar an ambaci wannan suna babu abin da zai fado ran mutane sai ce-ce-ku-ce saboda kurar da mai sunan ta tayar a shekarar 2016 lokacin da aka nuna ta a wani bidiyon waka tana "rungumar" wani mawaki.
Wannan batu dai ya jawo hankalin duniya musamman saboda caccakar da aka rika yi wa jarumar ta fina-finan Kannywood, abin da ya kai ga "korarta" daga yin fina-finan na Hausa.
Sai dai a zahiri Rahama Sadau, wacce ta soma taka rawa a fina-finan Kannywood a shekarar 2013, mace ce mai kamar maza, kamar yadda a duk lokacin da muka hadu take gaya min.
"Ni fa mace ce jaruma wadda idan na sa abu a gaba sai na kammala shi domin babu abin da ke dakatar da ni daga son cika burina".
Mene ne burinta?
A wata hira ta musamman da na yi da ita a shekarar 2015, jarumar ta shaida min cewa "babban burina shi ne na taka rawa a matsayin jaruma a dukkan manyan bangarorin fina-finan da ake yi a duniya: Hollywood, Bollyywood, Kannywood da kuma Nollywood".
Ta kuma jaddada min shaukinta na cika wannan buri nata a tattaunawar da muka yi a ranar Alhamis din da ta gabata.
Tun da ta soma fitowa a fina-finan Kannywood take hankoron baza komarta kuma tun ma kafin a "kore" ta daga Kannywood ta soma fitowa a fina-finan Nollywood da ake yi a kudancin Najeriya.
Sai dai babu ko shakka hanawar da aka yi mata fitowa a fina-finan Kannywood ta zamar mata tamkar gobarar Titi a Jos.
Jim kadan bayan haka ne fitaccen mawakin nan kuma jarumin fina-finan Hollywood Akon ya gayyace ta birnin Los Angeles na Amurka domin share mata hawaye.
A can ne kuma ta fito a wani fim din Hollywood wanda shi Akon din ya bayar da umarnin hadawa.
"Na ji dadin zuwa Amurka domin kuwa na koyi abubuwa da dama a kan fina-finai. Na yi fitowa ta musamman a wani fim da Akon ya hada. Yanzu kuma ina shirin fitowa a wasu fina-finan na Hollywood. Hasalima jiya-jiyan nan wasu Amurkawa suka zo nan Najeriya inda za mu ci gaba da daukar wani fim", in ji tauraruwar.
'Babu wanda ya dakatar da ni'
Da yake Rahama Sadau na cikin jaruman da suka fito a fim din na Rariya, na tambaye ta ko an janye korar da aka yi mata daga Kannywood, sai dai ta ce dama can ba a kore ta ba.
"Ni fa babu wanda ya kore ni daga Kannywood. Har yanzun nan babu wanda ya aiko min da wata takarda da ke nuna cewa an sallame ni daga Kannywood.
An rage ganina a fina-finan ne saboda, kamar yadda na gaya maka, ina fitowa a fina-finan Nollywood da kuma gudanar da sauran al'amuran rayuwata.
Amma yanzu zan koma yin fina-finan na Hausa gadan-gadan musamman ganin irin nasarar da fim dina na Rariya ya yi. Zan ci gaba da daukar nauyin fim baya ga fitowa a ciki da zan ci gaba da yi", in ji jarumar.
Na fahimci cewa akwai wata fahimtar juna a tsakanin kungiyar MOPPAN da ke sa ido kan masu shirya fina-finan Kannywood da Rahama Sadau ta yadda za ta janye jikinta daga fitowa daga fina-finan na Hausa, alabashi su kuma su bar ta ta koma fita a fina-finan bayan wani lokaci, musamman idan mutane suka soma mantawa da abubuwan da suka faru.
Da na tambaye ta kan ko ta yi da-na-sanin fitowa a bidiyon wakar da ya janyo ce-ce-ku-ce, Rahama Sadau ta yi murmushi sannan ta ce "kar ka manta na bai wa magoya bayana hakuri saboda abin da ya faru. Amma daga haka ba zan sake cewa komai ba".
Ganawa da Priyanka Chopra
Ita dai Rahama Sadau, wacce ke "jin" yaren Hindu kamar Amitabh Bachchan, ta shaida min cewa ta soma sha'awar fitowa a fina-finai ne saboda kaunar da take yi wa fittacciyar jarumar Bollywood, Priyanka Chopra.
"Tun ina karamar yarinya nake kallon fina-finan India kuma su ne ma suka yi gagarumin tasiri a rayuwata. Watakila hakan ba zai rasa nasaba da son fina-finan na India da mahaifina ke yi ba: ya je kasar India tun muna yara kuma shi ne ya soma koya min Indiyanci. Amma a dukkan jaruman fina-finan India babu wadda na fi kauna kamar Priyanka Chopra: mace ce jaruma, hazika kuma kuli-kuli ce mai sa gabanta inda take so," in ji jarumar.
Rahama Sadau ta ce takan yi wa Priyanka Chopra magana a shafukan sada zumunta akai-akai domin bayyana mata irin kaunar da take yi mata.
"Karon farko da na yi mata magana a Twitter shi ne a 2013, sai kuma a 2015 da kuma shekaranjiya [Talata]. A karon farko ba ta ce min komai ba; a karo na biyu kuma ta tambaye ni ni wace ce sai na gaya mata cewa ni jarumar fina-finan Hausa ce da ke matukar kaunarta.
Amma shekaranjiya da na yabi wani abu da ta wallafa a Twitter sai kawai ta ce min ta gode kuma tana fatan za mu hadu nan ba da dadewa ba. Hakan ya sa na ji dadi sosai", a cewar Sadau.
Yanzu dai jarumar ta ce ta samu hanyar ganawa da tauraruwar da take kauna kuma "na daure jakata ina jiran ranar da za ta ce min na hawo jirgi mu hadu da ita a koina ne kuwa a duniya. Wannan shi ne daya daga cikin manyan burikana".
Rariya
Baya ga fitowa a fina-finan da take yi, jarumar ta dauki nauyin hada fim na kanta a karon farko mai suna Rariya.
Fim din, wanda ya hada fitattun jaruman Kannywood irin su Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Fati Washa da Maryam Booth, ya karbu sosai a wurin masu kallo.
A cewar Rahama, "Na dauki nauyin fim dinne domin na fadada ilimina a fannin fina-finai sannan na samarwa matasa karin aikin yi. Fim din yana magana ne kan irin sakacin da iyaye ke yi na rashin kula da ya'yansu da ke karatun jami'a.
Za ka ga mahaifi ya bar 'yarsa a jami'a ba tare da yana sanya mata ido ba. Wani lokaci ma 'yar ce ke ciyar da gidansu kuma babu wanda ke tambayarta inda take samun kudi.
Yawanci za ka ga Alhazan birni da lakcarori sun lalata 'yarka kafin ka ce kwabo. Kuma wannan ya samo asali ne saboda rashin kulawar iyaye. Shi ya sa na ga ya kamata a fadakar da su".
Wani abu kuma da fim din na Rariya ya fito da shi, a cewar Rahama, shi ne irin kyashi da bakin kishin da ke tsakanin mata 'yan jami'a ta yadda wata za ta iya halaka wata idan ta ga ta fi ta samun abun duniya.
Rahama Sadau za ta gana da Priyanka Chopra ta India
Abin da ya fito fili game da rayuwar Rahama Sadau shi ne, kamar yadda ta fada, ita mace ce da ka iya shafe tsawon lokaci tana taka rawa a fina-finai da ma sauran al'amuran rayuwa, musamman ganin cewa baya ga fina-finan, tana yin wasu harkoki na wayar da kan jama'a kamar shirinta na kamfe a kan yaki da cutar daji da kuma kasuwanci.
Akwai rashin jituwa tsakanin Buhari da Saraki?

Adam A Zango ya gagari hukuma

Shahararren jarumin nan na fina-finan Hausa Adam Zango ya nuna wani bangare na fim dinsa 'Gwaska Return' kuma ya ce fin din yana shirin fitowa a shekara mai kamawa.
An hana ni aure saboda zargin luwadi - Adam A Zango
Ashe ba a dakatar da Rahama Sadau daga Kannywood ba?
Labarai masu alaka
Kannywood Najeriya

Shugaban kasar Nigeria Muhammad buhari ya bada kwangilar hanyar.........,..................... Kano

Gwamnatin Shugaba Buhari ta bayar da kwangilar hanyar Abuja-Kaduna-Kano wadda rashin bayar da kwangilar gina ta ta janyo wa gwamnatinsa suka a baya.
A wata zaman majalisar zartarwar kasar da aka yi tsakanin ranar Laraba zuwa ranar Alhamis ne aka bayar da kwangilar wadda aka bayar kan kudi naira biliyan 155 da miliyan 700.
Ministan ayyuka da gidaje da wutar lantarki, Babatunde Raji Fashola, ne ya fitar da sanarwar bayar da kwangilar.
Fashola ya ce majalisar zartarwar ta bayar da kwangilar babbar hanyar da ta tashi daga Efire zuwa Araromi da Aiyede da Aiyela wadda za ta hada jihar Ondo da ta Ogun akan kudi naira biliyan 14 da miliyan 400.
Har wa yau an gyara yawan kudin da za a kashe wa hanyar Inugu zuwa Anacha ta bangaren yankin Amansiya a kudu maso gabashin Najeriya.
Majalisar ta amince da ta bayar da kwangilar aikin hanyar da ke yankin Umunya a kudu maso gabashin Najeriyar kan Naira biliyan 23 da miliyan dari 400.
Gwamnatin Shugaba Buhari dai ta sha suka a baya game da irin abin da ya yi wa al'ummar jahar Kano, jahar da ta fi ba shi kuri'u a zaben da aka yi a shekarar 2015.
Kalli hotunan ziyarar Buhari a Kano
Buhari ya kara wa shugabannin soji wa'adin shugabancinsu
Majalisar Shari'a ta soki Buhari kan kin zuwa taro kan Kudus

Monday, 18 December 2017

Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure

Wata Amarya da aka yi ma auren dole, Shafa Muhammad mai shekaru 28 ta kai ma mijinta Umar Sheu mummunan hari da reza sati uku kacal da yin aurensu, inji rahoton Daily Trust.

Wannan lamari ya auku ne a daren juma’a 15 ga watan Disamba, a gidan ma’auratan dake Arkilla Liman, cikin karamar hukumar Wammako, a lokacin da mijin yaso yayi mu’amalar aure da Shafa.

Wani shaidan gani da ido ya shaida ma majiyar NAIJ.com cewa “Mijin na ta yayi kokarin saduwa da ita ne a lokacin da kai masa hari da reza dake ajiye a gefenta, nan take ta tatstsaga masa kai.”

Kaakakin rundunar Yansandan jihar Sakkawato, Ibrahim Abarass yace tuni aka garzaya da mijin zuwa Asibiti, inda ya samu kyakkyawan kulawa, kuma har an sallame shi.

Kaakakin yace sun kama uwargida Shafa, kuma zasu gurfanar da ita gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike akan lamarin. daga karshe ya shawarci iyaye da su guji yi ma yayansu auren dole.

Sunday, 17 December 2017

Rahama Sadau ta tsallake rijiya ta baya


Shahararriyar jarumar wasan Hausa, Rahama Sadau, ta sha da kyar a hannun wasu daliban jami'ar Umaru Musa dake jihar Katsina.
Tun farko shugabannin kungiyar daliban jami'ar ne suka gayyaci jarumar domin karramata a ranar Mata ta duniya. Saidai lamarin ya kwacube bayan isowar jarumar harabar taron, Students Centre, dake cikin jami'ar. 
Majiyar mu ta bayyana mana cewar jarumar ta iso wurin taron a makare, kuma zamanta keda wuya a teburin manyan baki sai dalibai suka barke da sowa da murnar ganin jarumar. Dalibai da dama sun nufi jarumar domin samun damar daukan hoto da ita, lamarin da ya kai an kasa sarrafa dandazon matasa masoya ga jarumar dake son yin hoton da ita.
Rahoton da muka samu ya tabbatar mana da cewar wasu daga cikin daliban ba iya son daukan hoto ya kai su ga wurin da jarumar ke zaune ba. Majiyar mu ta shaida mana cewar wasu daliban sun so afkawa jarumar ba don jami'an tsaro sun yi gaggawar shiga tsakani ba.
Da kyar jami'an tsaron jami'ar suka yi nasarar raba Rahama Sadau da janjamim masoyan dake ta kokarin kusantar ta da manufa daban-daban.
Babu rahoton samun lahani ko yin wata illa ga jarumar, an fitar da ita lafiya daga harabar jami'ar.
Kokarin Majiyar mu na jin ta bakin Jarumar ko kungiyar daliban jami'ar Umaru Musa yaci tura.
A satin da ya gabata ne jaruma, Rahama Sadau, ta yi bikin murnar zagayowar ranar haihuwar ta a kasar Cyprus.

Yadda aka 'tilasta wa' namiji fito da matar aure

Fitaccen daraktan fina-finan Kannywood Falalu A. Dorayi ya ce ya hada fim din "Auren Manga" ne saboda ya bai wa mutane dariya da sanya nishadi a zukatan masu kallo.
rahama sadau


A tattaunawarsa da Nasidi Adamu Yahaya, Baba Falalu, kamar yadda aka fi saninsa a Kannywood, ya ce ya gina maudu'in fim din ne domin ya sha bamban da sauran fina-finan barkwanci.
A cewarsa, "Na rubuta fim din "Auren Manga" ne sama da shekara biyar da suka wuce da zummar marigayi Rabilu Musa Dan Ibro ya zama babban jaruminsa, amma sai Allah ya yi masa rasuwa.
"Don haka ne na yi gyare-gyare a cikinsa kuma ni da kaina na zama babban jarumin cikin fim din".
"Babban abin da yake koyarwa shi ne yadda ake tilasta wa namiji, wato Manga ya fito da matar da zai aura. Ka ga hakan ya bambanta da yadda aka saba."
Falalu A. Dorayi ya ce mai daukar nauyin shirin Yakub Usman, ya kashe sama da naira miliyan biyu wurin hada fim din.
Fim din ya hada manyan jarumai irinsu Adam A Zango da Hadiza Gabon da Sulaiman Yahaya (Bosho) da Baban Chinedu da kuma Falalu Dorayi.

RIKICI YA YANKE A WANI YANKIN ABUJA

Wani rikici mai nasaba da kabilanci ya barke a garin Bwari da ke birnin tarayyar Najeriya, Abuja. Rikicin dai ya barke ne bayan wasu da a...